in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimman labarai daga wasu kafofin watsa labaran Najeriya
2016-10-27 19:16:40 cri
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon kwamitin da zai sanya ido game da ayyukan farfado da yankin arewa maso gabashin kasar, yana mai cewa an riga an gama da mafi muhimmancin aikin da aka sanya gaba game da yaki da kungiyar ta Boko Haram.

Shugaba Buhari wanda ya jagoranci kaddamar da kwamitin a jiya Laraba, ya ce a kalla mutum 20,000 ne suka rasa rayukan su, baya ga kimanin mutane miliyan 2.4 da suka rasa matsugunan su, kana an yi asarar biliyoyin Nairori sakamon ayyukan kungiyar. (Daily Trust)

Rundunar sojojin Najeriya na tsare da wasu jami'an ta biyu, masu mukamin manjo da kuma kyaftin, bisa zargin su da yiwa yakin da ake yi da 'yan Boko Haram kafar ungulu.

Wata majiyar rundunar ta tabbatar da cewa, mahukuntan ta sun dukufa wajen tabbatar da sun kakkabe bara-gurbi daga ayyukan yaki da 'yan ta'adda da rundunar ke aiwatarwa. (The Punch)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China