in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta tisa keyar bakin haure 53
2016-10-27 09:47:18 cri
Jami'in hukumar kula da shigi da fici ta Najeriya ya ce, kimanin bakin haure 53 ne gwamnatin kasar ta aza keyarsu zuwa jamhuriyar Nijer wadanda suka shigo Najeriyar ta haramtattun hanyoyi.

Tamuno Oyedeji, shi ne kwantirolan hukumar shigi da fice a arewacin jihar Niger, ya sheda wa 'yan jaridu a Minna cewa, an mayar da bakin hauren zuwa kasarsu ne saboda zamansu a jihar yana matukar yin barazana ga sha'anin tsaro ga Najeriyar.

Jam'in ya kara da cewa, hukumar tana ci gaba da daukar tsauraran matakai na tsaro, domin tabbatar da cewa wadanda ke da takardun izinin na hakika ne kadai za su iya shigowa kasar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China