in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Syria ta zargi Turkiyya da hallaka mutane 150 a wani hari ta jiragen sama a yankin Aleppo
2016-10-21 09:53:17 cri
Kamfanin dillancin labaran SANA ya rawaito cewa, dakarun sojin Syrian sun zargi Turkiyya da hallaka mutane 150 a wani hari da suka kaddamar ta jiragen saman yaki a arewacin birnin Aleppo.

Babban kwamandan dakarun sojin Syrian ya ce, Turkiyya ta kaddamar da hare hare ta sama a garuruwa da kauyuka a shiyyar arewacin lardin Aleppo inda ta hallaka fararen hula, kuma a cewar jami'in sojin wannan mataki yana kara dagula al'amurra game da halin da ake ciki a yankin.

A wani labarin kuma, dakarun sojin Syrian sun yi barazanar kakkabo jiragen saman Turkiyyar wadan da ke kokarin saba dokokin da suka shafi sararin samaniyar Syria.

Ya kara da cewa "duk wani yunkuri da jiragen yakin Turkiyya ke yi na saba dokokin sararin samaniyar Syria ba abin da za'a lamunce da shi bane".(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China