in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sake samun rikice-rikice bayan kammala wa'adin tsagaita bude wuta a Aleppo na kasar Syria
2016-10-23 13:17:50 cri
Bayan kammala wa'adim tsagaita bude wuta har na tsawon kwanaki 3 a kasar Syria, sojojin gwamnatin kasar da dakaru masu adawa da gwamnati sun sake yin musayar wuta a birnin Aleppo dake arewacin kasar a ranar 22 ga wata.

Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Syria suka bayar, an yi musayar wuta a gabashin birnin Aleppo da dakaru masu adawa da kungiyar masu tsattsauran ra'ayi da suke rike da yankin.

Wani hafsan sojojin gwamnatin kasar ya bayyana cewa, a yayin da ake tsagaita bude wuta na kwanaki uku, dakarun kungiyar Ahrar al-Sham guda 7 kawai sun mika wuya ga sojojin gwamnatin kasar, kana wasu fararen hula sun janye daga yankin gabashin Aleppo. Bangaren soja na kasar Syria ya zargi kungiyar masu tsattsauran ra'ayi da kawo cikas ga tsagaita bude wuta da janyewar fararen hula daga yankin.

Bangaren sojan kasar Syria ya sanar a daren ranar 19 ga wata cewa, an tsagaita bude wuta har na tsawon kwanaki 3 a Aleppo don tabbatar da janyewar dakaru masu adawa da fararen hula daga yankin gabashin birnin Aleppo. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China