A nasu bangare, shugaban kasar Syria Bashar al-Assad, da takwaransa na kasar Rasha, Vladimir Putin, sun zanta ta wayar tarho a ranar Laraba, don tattauna yanayin da ake ciki a kasar Syria ta fuskar yakar ta'addanci.
A yayin tattaunawarsu, kamar yadda kamfanin dillancin labaru na kasar Syria ya rawaito, shugaba Putin ya ce matsayin da kasar Rasha ta dauka dangane da batun Syria bai canza ba ko kadan, sa'an nan kasar za ta ci gaba da kokarinta na dakile ta'addanci, da kuma kare cikakken yankin kasar Syria.
A nasa tsokaci, shugaba Bashar na kasar Syria ya godewa kasar Rasha, kan irin taimakon da ta baiwa kasar sa. A cewarsa, Syria ta dau niyyar murkushe ta'addanci a kasar, da neman samun masalaha tsakanin al'ummar kasar, ta yadda za a samu damar sake bude hanyar daidaita matsalar siyasar kasar ta hanyar shawarwari.(Bello Wang)