in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Syria:An sanar da tsagaita bude wuta a Aleppo
2016-10-20 13:25:02 cri
Gidan telabijin mallakar kasar Syria ya ba da labarin cewa, a daren ranar Laraba wasu sojojin bangare masu adawa da gwamnatin kasar ta Syria, sun fara janyewa daga gabashin birnin Aleppo, birnin da aka dade da yi masa kawanya. Sauran mutanen da suka fice tare da sojojin sun hada da wadanda suka jikkata, da marasa lafiya gami da tsofaffi.

Ban da haka kuma, sojojin kasar Syria sun sanar a daren ranar Laraba cewa, za a tsagaita bude wuta har tsawon kwanaki 3 a birnin Aleppo, tun daga karfe 8 safiyar ranar Alhamis bisa agogon wurin.

A nasu bangare, shugaban kasar Syria Bashar al-Assad, da takwaransa na kasar Rasha, Vladimir Putin, sun zanta ta wayar tarho a ranar Laraba, don tattauna yanayin da ake ciki a kasar Syria ta fuskar yakar ta'addanci.

A yayin tattaunawarsu, kamar yadda kamfanin dillancin labaru na kasar Syria ya rawaito, shugaba Putin ya ce matsayin da kasar Rasha ta dauka dangane da batun Syria bai canza ba ko kadan, sa'an nan kasar za ta ci gaba da kokarinta na dakile ta'addanci, da kuma kare cikakken yankin kasar Syria.

A nasa tsokaci, shugaba Bashar na kasar Syria ya godewa kasar Rasha, kan irin taimakon da ta baiwa kasar sa. A cewarsa, Syria ta dau niyyar murkushe ta'addanci a kasar, da neman samun masalaha tsakanin al'ummar kasar, ta yadda za a samu damar sake bude hanyar daidaita matsalar siyasar kasar ta hanyar shawarwari.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China