Babban jami'i mai kula da rundunar yaki ta kasar Rasha Sergey Rudskoy, ya ce ana sa ran za'a kaddamar da shirin bada agaji da misalin karfe 8 na safe zuwa 4 na yammacin ranar 20 ga watan nan da muke ciki, kuma a lokacin ne ake sa ran hukumar kula da jiragen saman yaki ta Rasha da dakarun gwamnatin Syria zasu dakatar da kai hare hare ta sama.
Ya kara da cewa, Rasha a shirye take ta tsakaita bude wuta, sannan ta bada dama ga jami'an kiwon lafiya su samu damar shiga birnin Aleppo kamar yadda hukumomin bada agaji suka bukata domin ceto marasa lafiya da wadanda suka jikkata.
Jiragen saman yakin Rasha da dakarun sojin gwamnatin Syria dake biyayya ga shugaba Bashar al-Assad na cigaba da yin luguden wuta a yankunan dake karkashin ikon 'yan tawaye a birnin Aleppo, tun bayan rushewar yarjejeniyar tsakaita bude wuta da aka cimma tsakanin Amurka da Rasha a watan jiya.(Ahmad Fagam)