A ran 13 ga watan nan da muke ciki, an bude babban taron MDD karo na 71 a hedkwatar MDD dake birnin New York na kasar Amurka, inda aka mai da taken babban taron bisa "burinmu na samun dauwamammen ci gaba, kyautata duniyar da muke zama cikin hadin gwiwa". Haka kuma, za a shirya mahawara na kowa na babban taron MDD na wannan karo tun daga ranar 20 zuwa ranar 26 ga watan nan, a lokacin kuma, shugabannin kasa da kasa za su ba da jawabi kan yadda za a nemi ci gaban duniya da kuma wasu al'amuran kasa da kasa wadanda suka fi janyo hankulan al'ummomin kasa da kasa.
Bugu da kari, Mr. Thomson ya ce, a lokacin da za a yi taron shugabannin babban taron MDD, zai halarci taron karawa juna sani kan yadda za a aiwatar da jadawalin neman dauwamammen ci gaba na shekarar 2030 da kasar Sin ta sa kaimi da za a gudana, inda zai kuma ba da jawabi. Kaza lika, a cewarsa, taron zai kasance wata babbar dama da za a ji ra'ayoyin shugabannin duniya kan yadda suke aiwatar da burinmu na neman dauwamammen ci gaba a yayin da suke neman ci gaba na kasarsu.
Mr. Thomson ya kara da cewa, kasar Sin ta taka mihimmiyar rawa wajen aiwatar da burin MDD na kawar da talauci, shi ya sa, muna fatan kasar Sin za ta ci gaba da kasancewa kan gaba a duniya wajen aiwatar da burin neman dauwamammen ci gaba. (Maryam)