in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya yi kira da kara sa ido kan batun cin zarafin mata da wasu sojojin wanzar da zaman lafiya na MDD suka yi
2016-09-08 16:02:49 cri
A jiya Laraba 7 ga wata, mataimakin zaunannen wakilin Sin a MDD, Wu Haitao ya bayyana cewa, kamata ya yi kasa da kasa su kara sa ido kan batun cin zarafin mata da wasu sojojin wanzar da zaman lafiya na MDD suka yi.

A wannan rana, an kira babban taron MDD kan batun cin zarafin mata da wasu sojojin wanzar da zaman lafiya na MDD suka yi. A yayin da yake jawabinsa, Wu Haitao ya bayyana cewa, a cikin 'yan shekarun da suka wuce, wasu sojojin wanzar da zaman lafiya kadan ne suka ci zarafin mata a wasu kasashen duniya, wannan ya ci amanar aikin kiyaye zaman lafiya da ta MDD. Kamata ya yi bangarori daban daban su daina yin hakuri kan wannan danyen aiki, su yi rigakafi tare da gurfanar da wadanda suka aikata laifin cin zarafin mata a gaban kotu, domin kiyaye sunan MDD da bunkasuwar aikin kiyaye zaman lafiya na MDD yadda ya kamata.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China