A yayin taron manema labaru da ma'aikatar tsaron kasar Sin ta gudanar a yau Alhamis, kakakin ma'aikatar Yang Yujun, ya bayyana cewa, Sin za ta kammala rajistar sojojin kiyaye zaman lafiya 8000, wadanda ke jiran ayyukan da za su gudanar karkashin MDD.
Mr. Yang ya bayyana cewa, bayan taron koli na kiyaye zaman lafiya na MDD da aka gudanar a bara, sojojin kasar Sin sun riga sun horar da ma'aikata masu aikin kiyaye zaman lafiya kimanin 500 na kasashen duniya da dama. Kaza lika an shirya tura rukuni na farko na jiragen sama masu saukar ungulu, na kiyaye zaman lafiya zuwa bakin aiki.
Hakazalika kuma, Sin tana tattaunawa tare da kungiyar AU, game da shirin bada gudummawar kudi, da yawansu ya kai dala miliyan 100 cikin shekaru 5 masu zuwa. Mr Yang ya kara da cewa, a matsayin babbar kasa mai sauke nauyin dake wuyan ta, Sin za ta ci gaba da cika alkawarinta na gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiyar MDD, da taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye zaman lafiya a duniya baki daya. (Zainab)