A daren jiya Litinin, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da babban magatakardan MDD Ban Ki-moon a birnin New York na kasar Amurka.
A yayin ganawar tasu, Li Keqiang ya ce, kasar Sin tana son ci gaba da goyon bayan MDD ta yadda za ta ba da gudummawa kan aikin kiyaye zaman lafiya da ci gaba a duniya.
A nasa bangare kuma, Ban Ki-moon ya ce, MDD ta nuna yabo matuka kan kokarin da kasar Sin take yi da kuma babbar gudummawar da take bayarwa wajen tinkarar sauyin yanayi, kara azama kan neman dauwamammen ci gaba, karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa da kuma gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya na duniya da dai sauransu, kana, tana son ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasar Sin wajen tinkarar kalubalolin dake gaban bil Adama da kuma ciyar da zaman lafiya da ci gaban duniya gaba. (Maryam)