Bisa labarin da aka samu daga gidan talabijin na jamhuriyar Kamaru, an ce, an kawo karshen aikin ceto a yankin Eseka dake tsakiyar kasar, bayan hadarin da ya faru ne sakamakon gocewar jirgin kasa daga layinsa a ranar 21 ga wannan wata, kawo yanzu an fara gudanar da bincike game da musabbabin da ya haddasa hadari a hukumance.
Hadarin dai ya haddasa rasuwar mutane 80, yayin da mutane sama da 500 suka jikkata.
Gwamnatin kasar ta ayyana ranar Litinin da ta gabata a matsayin ranar ta'aziya a duk fadin kasar, kuma an sauke rabin tutar kasar domin nuna juyayi ga wadanda suka rasa rayukansu a sanadiyyar hadarin jirgin kasan. (Maryam)