Gidan rediyon jamhuriyar Kamaru ya ba da labarin cewa, a jiya Jumma'a an samu mummunan hadarin jirgin kasa a tashar jirgin kasa ta Eseka dake tsakiyar jamhuriyar Kamaru, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 53, a yayin da mutane 300 suka jikkata.
Ministan zirga-zirga na kasar Kamaru Edgar Alain Mebe Ngo'o da sauran jami'an hukumar jiragen kasa ta kasar, sun ziyarci wurin da lamarin ya faru.
Bisa wani labari na daban da aka bayar, an ce, wani sashe na hanyar da ta hada biranen Yaounde da Douala ya lalace, a sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka samu a safiyar wannan rana, lamarin da ya sa fasinjoji da dama suka yanke shawarar shiga jiragen kasa a maimakon motoci. Sakamakon karin mutanen da aka samu, hukumar zirga-zirgar jiragen kasar suka kara yawan taragu, yawan fasinjojin da jiragen kasan suka dauka ya ninka sau biyu idan aka kwatanta da wanda suka saba dauka yau da kullum.
Wani mutumin da ya ganewa idonsa faruwar lamarin ya ce, jirgin kasa ya kauce daga layin dogo ne a lokacin da yake shirin shiga tashar jirgin kasa ta Eseka, hakan ne ya haddasa hadarin wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. (Lami Li)