An ce a jiya Lahadi, jami'an dake aikin ceto sun fiddo karin wasu gawawwaki daga sassan jirgin da ya sauka daga hanyar sa, kwanaki biyu bayan hadarin da ya auku a tashar Eseka, mai nisan kilomita 120 daga kudu maso yammacin birnin Yaounde fadar mulkin kasar.
Baya ga wadanda suka rasa rayukan su, wasu karin mutanen kimanin 600 na jiyya a asibitoci daban daban, sakamakon hadarin da ya rutsa da su.(Saminu Alhassan)