Shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya bayyana a ranar 22 ga wata cewa, mutane a kalla 70 sun mutu a sakamakon hadarin, tare da raunatar mutane 600, kuma ya nuna ta'aziyya ga mutanen da suka mutu a sakamakon hadarin.
Shugaba Biya ya bukaci gwamnatin kasar da ta dauki matakai don samar da gudummawa ga iyalan mutanen da suka mutu da wandanda suka ji rauni a sakamakon hadarin, da bada umurni ga hukumomin da abin ya shafa da su yi bincike kan dalilin abkuwar hadarin.
Mista Biya ya sanar da sanya ranar 24 ga wannan wata a matsayin ranar zaman makoki a kasar, a lokacin hukumomin kasar da ma'aikatun jakadancin kasar dake kasashen waje za su saukar da tuta zuwa rabin sanda don nuna juyayi.
Wani jirgin kasa wanda ya tashi daga birnin Yaounde na kasar Kamaru zuwa birnin Douala na kasar ya kauce daga layin dogo a yankin Eseka a ranar 21 ga wata, yanzu masu bada ceto suna neman gawawwakin mutanen da suka mutu, da kai wadanda suka ji rauni zuwa asibiti. (Zainab)