A cewar sanarwar MDD ta ranar Alhamis, mista Ban ya gabatar da ta'aziyyarsa ga iyalan mutanen da suka rasa rayukansu, da jajantawa gwamnati da al'ummar kasar Kamaru. Tare da kuma fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata a yayin wannan hari.
Sakatare janar na MDD ya kara yin kira ga dukkan abokan hulda da su samar da taimako ga kungiyar tafkin Chadi da kuma Benin, tare da tallafin kungiyar tarayyar Afrika AU da kungiyar musamman ta hadin gwiwar kasa da kasa, domin dakile bazaranar da Boko Haram ke kawo a shiyyar.
Mutane goma sha daya suka mutu yayin da wasu hudu suka samu rauni mai tsanani a lokacin harin kunar bakin wake ya faru a cikin daren Laraba zuwa Alhamis a Limani, wani birnin dake kuriyar arewacin Kamaru mai iyaka da Najeriya. (Maman Ada)