in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masana: Nasarar Sin ta dogara ga jagorancin JKS
2016-10-24 10:48:45 cri
A yau Litinin ne, aka bude cikakken zaman taro na 6 na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin karo na 18 a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, taron da ake fatan kammala shi a ranar 27 ga wannan wata.

Mahalarta taron za su yi nazari game da yadda za a gudanar da harkokin jam'iyyar kwaminis ta Sin ba tare da sakaci ba, ta hanyar tsara wasu ka'idojin jam'iyyar kwaminis ta Sin ta fuskar harkokin siyasa, da kuma gyara ka'idojin sa ido kan harkokin 'yan jam'iyyar kwaminis ta Sin, lamarin da ya nuna aniyar kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta Sin wajen gudanar da harkokin jam'iyyar ba tare da nuna sakaci ba. Daukar wannan mataki, ya sa jami'ai da masana dake shafar harkokin jam'iyyu na kasashen ketare suke mai da hankali matuka kan wannan taron da ake yi a halin yanzu a nan birnin Beijing, sun kuma nuna yabo da amincewa kan matakan da jam'iyyar kwaminis ta Sin ta dauka wajen gudanar da harkokinta ba tare da nuna sakaci ba. Suna mai cewa, lamarin zai kara taimakawa jami'yyar kwaminis ta kasar Sin wajen cimma nasarorin da ta sanya a gaba.

Tsohon mataimakin ministan harkokin wajen kasar Masar Ahmad Wali ya ce, cikakken zaman taro na 6 na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin karo na 18 ya mai da hankali kan gudanar da harkokin jam'iyyar kwaminis ba tare da nuna wani sakaci ba, inda kuma za su gudanar da bincike kan muhimman takardun ka'idoji da manufofin jam'iyyar kwaminis ta Sin, lamarin da zai taimaka wa jam'iyyar kara inganta ayyukanta na ginawa da sa ido kan harkokin jam'iyyar kwaminis ta Sin, ta yadda za a kara inganta matakan tafiyar da jam'iyyar.

Kaza lika, ya ce, shirin zirin tattalin arziki na siliki da hanyar siliki ta ruwa na karni na 21 da kasar Sin ta bullo da su, ya samar wa kasar Masar da sauran kasashen da abin ya shafa sabbin damamakin samun bunkasuwa. A saboda haka, ana fatan jam'iyyar kwaminis ta Sin za ta ci gaba da aiwatar da matakan yaki da cin hanci da karbar rashawa da ta ke gudanarwa, domin tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikin kasar cikin sauri da kuma karko, ta yadda hakan zai taimaka wa kasashen duniya wajen cimma bunkasuwar tattalin arziki cikin hadin gwiwa.

Shehun malami a jami'ar dangantakar kasa da kasa ta Amurka na birnin Nairobi na kasar Kenya Macharia Munene ya bayyana cewa, lokacin da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta kira cikakken zaman taronta karo na farko, adadin 'yan jam'iyyar bai wuce dari daya ba, amma a halin yanzu, yawan 'yan jam'iyyar ya kai sama da miliyan 80, lamarin da ya nuna muhimmiyar rawar da jam'iyyar ta taka kwarai da gaske, haka kuma, ana iya cewa, jam'iyyar kwaminis ta Sin tana ci gaba da samun bunkasuwa cikin sauri yadda ya kamata. Haka kuma matakan yaki da cin hanci da karbar rashawa da jam'iyyar ta ke aiwatarwa sun samu yabo da amincewar Sinawa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China