in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsakiyar JKS ya kira taron yin shawarwari tsakaninsa da mutanen da ba membobin JKS ba
2016-07-26 20:21:58 cri
A jiya Litinin ne, kwamitin tsakiyar jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) ya kira taron yin shawarwari tsakaninsa da mutanen da ba membobin JKS ba a birnin Beijing, inda aka saurari ra'ayoyi da shawarwari daga wakilan wasu jam'iyyun Sin da wadanda ba sa cikin kowace jam'iyya dangane da yanayin da tattalin arzikin Sin ke ciki da aikin raya tattalin arziki a watanni shida na karshen wannan shekara.

A jawabin da ya gabatar yayin taron shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bayyana cewa, bana shekara ce ta cika shekaru 95 da kafa jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana shekarar farko da aka fara aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 13, a sabili da haka, gudanar da aikin raya tattalin arziki yadda ya kamata, da sa kaimi ga bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma na da muhimmanci kwarai da gaske.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China