Dr. Robert L. Kuln na kasar Amurka kana masani kan harkokin Sin ya ce, yana goyon bayan shirin kasar na bude kofa ga kasashen wajen da yin kwaskwarima cikin gida da ake aiwatarwa karkashin jagorancin JKS. A ganinsa, wannan shiri ya samarwa kasar kudade da dama a cikin gajeren lokaci, kana ya kawar da Sinawa fiye da miliyan 5 daga kangin talauci, wannan abin al'ajabi ne.
Ya kuma nuna rashin amincewa da yadda yammacin kasashen duniya ciki har da kasar Amurka suke yiwa JKS bahaguwar fahimta. Ya ce, jama'ar kasar Sin sun zabi JKS da tsarin gurguzu, wanda ya dace da yanayin Sin da bunkasuwarta.
Shi ma shugaban cibiyar nazarin harkokin da suka shafi Sin da kudancin Afirka ta kasar Zimbabwe Phyllis Johnson ya bayyana cewa, JKS ta taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa kasar Zimbabwe wajen samun 'yancin kai. Ko da yake jama'ar kasar Zimbabwe su ne suka kwatawa kasarsu 'yancin kai, amma sun samu goyon baya daga sauran kasashen duniya, kuma, Sin ta taka muhimmiyar rawa. A karnin 21, shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya kaddamar da manufar koyon fasahohin Sin da manufofin JKS. A ganin Phyllis Johnson, JKS tana da fasahohi da suka shafi tafiyar da harkokin kasa, ya kamata Zimbabwe ta koye su. (Zainab)