Gwamnatin kasar Sin ta kuduri aniyar zamanantar da aikin noma a dukkanin fadin kasar nan da shekara ta 2020. Haka dai na kunshe ne cikin wani sabon tsarin shekaru biyar, wanda majalissar zartaswar kasar ta fitar a ranar Alhamis.
Manufar tsarin dai ita ce samar da isasshen abinci, da tabbatar da ingancin kayayyakin abincin, tare da karfafa gogayyar kasar ta fuskar samar da abinci nan da shekara ta 2020.
Har wa yau tsarin zai baiwa mazauna yankunan karkara damar gudanar da ingantacciyar rayuwa daidai misali, za kuma a yi amfani da shi wajen kafa cibiyoyin gwajin ayyukan gona na zamani a sassa daban daban.
Kaza lika tsarin zai taimaka wajen inganta ayyukan kirkire-kirkire, da na gudanarwa, tare da samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, baya ga batun bude kofofin ci gaba ga manoma. (Saminu)