Cibiyar inganta masara da alkama ta duniya da abokan huldarta sun kaddamar da shirin STMA wanda zai rage wahalar da ake fuskanta a noman masaran da ya danganci yanayi wanda yake aukuwa a duk lokacin da ya kama a yankuna da dama a Nahiyar.
A karkashin shirin an samar da sabo da kuma ingantaccen dabaru da iri da za su jure da sajewa da yanayin rashin ruwa, karancin kasa mai fidda shuka, zafi, cututtuka kamar mai lalata masara da kwari.
Fiye da hekta miliyan 35 na gonar masara a Hamadan Afrika suke bukatar ruwan sama, kuma suke fuskantar barazana sakamakon sauyin yanayi, abin da ke haifar da yawan fari a gonakin manoma.
A lokaci daya kuma noman masaran ya ragu saboda rashin kasa mai karfi da zai iya fidda tsiron shi a yawancin yankin na Saharan Afrika, sai dai kuma yawancin manoma masu karamin karfi ba su da iya samun isashshen takin zamanin da ya kamata.
Sakamakon haka, an kara samun matsaloli masu zamani wajen samar da hatsi, balle kudin kashewa, da isashshen abinci mai gina jiki ga miliyoyin manoma da iyalansu.
Shirin na tsawon shekaru 4 zai inganta samar da nau'o'in masara daga wajen kusan magidanta miliyan 5 da rabi nan da karshen shekara ta 2019. (Fatimah Jibril)