Kasar Togo ta bayyana niyyarta ta kafa wani yankin bunkasa albarkatun noma na farko a cikin watan Febrairun shekarar 2017 a yankin Kara dake arewacin kasar, tare da taimakon kudi daga bankin ci gaban Afrika (BAD), in ji gwamnatin Togo a ranar Talata.
Burin na shugabannin Togo shi ne na gina wani muhimmin yankin noma tare da dora muhimmanci sosai wajen sarrafawa albarkatun noman ta hanyar fasahohin zamani, in ji gwamnatin. (Maman Ada)