Masanan sun yi wadannan kamalai a ranar Litinin a yayin wani dandalin kasa da kasa game da nagartattun matakai ta fuskar zuba jarin karkara da noma a Kigali, hedkwatar kasar Rwanda.
Haduwar ta ranar 1 zuwa 3 ga watan Augusta, na da taken "Sanya ido cikin sauri game da yiyuwar aiki da sabbin hanyoyin zuba jarin karkara da noma".
Taron, dake mai da hankali kan matakan bunkasa samar da zuba jari ga noma a cikin kasashe masu tasowa, ya tattara kwararru fiye da 250 da masu ruwa da tsaki na kasa da kasa, shiyoyi da na cikin gida a fannin zuba jarin karkara da noma.
Saleh Usman Gashua, sakatare janar kungiyar bada rancen karkara da noma a Afrika (AFRACA), ya bayyana a yayin wannan taro, cewa zuba jarin da bai dace ba a cikin ayyukan noma a yawancin kasashen Afrika na kasancewa wata barazana ga ci gaban bangaren noma.
Masu zuba jari a Afrika na mayar da hankali kan daidaita hanyar zuba jarinsu a cikin ma'adinai, makamashi da ci gaban ababen more rayuwa, tare da barin bangaren noma a baya. Hukumomin kudi su ma ba su taimakawa manoma ba domin sharuda da matakan samun kasance masu wuya ga kananan manoma wajen samun rancen kudi, in ji mista Gashua. (Maman Ada)