in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta shawarci Afirka da ta rungumi tsarin noma na zamani
2016-09-29 20:05:27 cri
Hukumar abinci da aikin gona ta MDD FAO, ta yi kira ga kasashen dake kudu da hamadar saharar Afirka, da su rungumi tsarin noma na zamani, matakin da zai zamo hanyar warware matsalar kamfar abinci, tare da bunkasa rayuwar al'ummun karkara.

Wannan kira dai na kunshe ne cikin wani rahoto da hukumar FAO ta fitar a Alhamsi din nan. FAO ta ce amfani da na'urorin zamani na inganta noma, da bin kyawawan tsare tsare, za su taimaka matuka wajen ciyar da dunbin jama'a dake wannan yanki.

Da yake karin haske game da hakan, mataimakin babban daraktan hukumar ta FAO, kuma shugaban sashen noma da kariya ga masu sayayya Ren Wang, ya ce idan har aka dauki wannan mataki, ko shakka babu, hakan zai sauya tsarin cin gajiyar albarkatun noma a yankunan kudu da hamadar Sahara, ta yadda miliyoyin al'ummun karkara za su amfana.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China