Shugaba Zuma ya bayyana hakan ne a birnin Durban, yayin taron gamayyar kungiyoyin 'yan kwadago na duniya, wanda ya gudana a jiya Laraba. Ya ce taron na bana na gudana a wani lokaci da ake fuskantar tarin matsaloli na tattalin arzikin duniya.
Sai dai duk da haka a cewar sa, muddin Afirka ta Kudu ta samu karin kaso daya bisa dari na ci gaba a shekara mai zuwa kamar yadda aka yi hasashe, hakan zai bada damar samar da guraben ayyukan yi sama da 80,000, yayin da karuwar kaso 3 bisa dari za ta haifar da guraben ayyukan yi 300,000.
Don haka shugaba Zuma ya jaddada kudurin gwamnatin sa na daga matsayin mizanin ci gaban kasar, kamar yadda hakan ke kunshe cikin sabon tsarin bunkasa kasar na shekaru masu zuwa.(Saminu Alhassan)