Brigadier Hangwani, kakakin kungiyar Hawks da ke kula da manyan batutuwan shari'a na 'yan sandan kasar, ya bayyanawa kafofin watsa labarai cewar, ana tuhumar wadannan mutane hudu da yunkurin shirya harin ta'addanci a birnin Johannesburg, wadanda shekarunsu suka kai 20 zuwa 25 da haihuwa.
Haka kuma Mr. Hangwani ya ce, wannan aikin kama masu aikata laifi da kungiyarsa ta Hawks ta gudanar ya samu taimako ne daga hukumar tsaron lafiyar kasar Afirka ta Kudu, da kungiyar kau da boma-bomai, da sauran hukumomin aiwatar da doka. Bisa binciken da aka yi, an ce, a shekarar 2015, wadannan mutane hudu sun taba nuna aniyar zuwa kasar Sham don shiga kungiyar IS mai tsattsauran ra'ayi, kuma tun daga wancan lokaci ne, 'yan sanda suka fara bincikensu.
Shugaban kungiyar Hawks Mthandazo Ntlemeza, ya kuma furta a ran nan cewar, kama wadannan mutane hudu wani babban ci gaba ne da kasar Afirka ta Kudu ta samu wajen yaki da ta'addanci. Ya kara da cewa, kasar Afirka ta Kudu za ta kiyaye matsanancin tsaro, a kokarin murkushe kowace irin makarkashiyar ta'addanci da za a shirya a kasar. (Kande Gao)