Shugabannin jami'ar Wits sun tabbatar da cewa, galibin daliban jami'ar sun jefa kuri'un amincewa don kawo karshen boren nasu ta hanyar aikewa da sakon wayar salula.
Kafin haka an riga an dakatar da dukkan ayyuka masu alaka da karatu da nazari a jami'ar har tsawon mako daya, sakamakon zanga-zangar da daliban jami'ar suka gudanar don nuna kin amincewarsu kan bukatar gwamnati ta kara kudin karatu.
Blade Nzimande, ministan ilimin kasar Afirka ta Kudu, ya bada umurni a makon da ya gabata cewa, jami'o'i za su iya kara kudin kararun da dalibansu suke biya, idan karin ba zai wuce kashi 8 cikin 100 ba. Wannan mataki ya sa daliban kasar na jami'o'i daban daban gudanar da zanga-zanga.(Bello Wang)