Dalibai sun yi watsi da haramcin da 'yan sanda suka yi musu na yin zanga zanga, cewa ba su da ikon nuna adawa kan karin kudin karatu.
Zanga zangar ta yi muni duk da cewar yawancin dalibai sun jefa kuri'a domin komawa karatu a ranar Litinin.
A makon da ya gabata yawancin dalibai na jami'ar Wits sun jefa kuri'ar kawo karshen zanga zanga ta hanyar aike da sako kan wayarsu.
'Yan sandan sun bayyana cewa sun harbe harsasai na roba da gurmeti mai sa kyalla bayan da dalibai suka kai musu hari da duwatsu. Daruruwan dalibai ne suka yi jerin gwano a cikin jami'ar a lokacin da aka turo 'yan sanda domin su kwantar da tarzomar.
A ranar Talata, zanga zangar dalibai sun gudana a cikin jami'ar Cap da sauran hukumomin ilimi mai zurfi na kasar.
Dukkan ayyukan karatu na jami'ar sun tsaya a tsawon kusan mako guda a cikin yawancin manyan jami'o'in kasar dalilin zanga zangar nuna adawa da karin kudin karatu.
Zanga zangar sun barke a karshen watan da ya gabata a yayin da ministan ilimi mai zurfi, mista Blade Nzimande, ya sanar da cewa jami'o'in kasar suna iya kara kundin karatunsu a shekarar 2017, idan har karin ba zai wuce kashi 8 cikin 100 ba. (Maman Ada)