Shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Afrika ta Kudu, Jacob Zuma, sun sanar da wannan mataki a yayin tattaunawarsu a dab da taron BRICS, wato gungun dake kunshe da kasashen Brazil, Rasha, Indiya, Sin da Afrika ta Kudu.
Shugabannin kasashen biyar zasu tattauna kan dangantakarsu bisa tsarin BRICS, da kuma sauran batutuwan dake janyo hankalinsu a yayin wannan dandali da za a gudanar daga ranar 15 zuwa 16 ga watan Oktoba, bisa taken "Bullo da hanyoyin da suka dace, daga dukkan fannoni kuma cikin hadin gwiwa".
Shugaban kasar Sin ya isa a ranar Asabar da rana a jihar Goa ta Indiya dake yammacin kasar domin halartar dandalin BRICS. Kasar Indiya shi ne zango na karshe na ziyararsa a kudu maso gabashin Asiya da kudancin Asiya, bayan da tuni ya kai ziyara a kasashen Cambodia da Bangladesh. (Maman Ada)