A yayin ganawar tasu, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar Sin tana godiya matuka dangane da goyon bayan da kasar Banglagesh take bata domin kiyaye muhimman moriyar kasar Sin, haka kuma, tana goyon bayan kasar Banglagesh kan harkokin kiyaye 'yancin kanta da mulkin kasa, sa'an nan, Sin ta amince da kokarin da kasar Banglagesh ta yi wajen tabbatar da zaman lafiya da kuma neman cigaban kasar. Haka zalika, shugaba Xi ya kara da cewa, kamata ya yi kasashen biyu su ci gaba da karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu domin aiwatar da ayyukan shirin neman dauwamammen cigaba nan da shekarar 2030 kamar yadda aka tsara, da kuma ciyar da hadin gwiwar kasashe masu tasowa gaba.
A nasa bangaren, shugaba Abdulla Hammed ya ce, kasarsa zata cigaba da nuna goyon baya ga kasar Sin kan harkokin kiyaye muhimman moriyar kasashen biyu, kuma tana son zama abokiyar hadin gwiwar Sin domin neman cigaba tare, kana da karfafa shawarwarin dake tsakanin kasashen biyu kan muhimman harkokin kasa da kasa da shiyya-shiyya. (Maryam)