Shugaban Xi wanda shi ne babban sakataren jam'iyyar kwaminis mai mulkin kasar Sin, ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa game da tsarin gudanar da mulki, sanarwar da kuma shugaban hukumar siyasa da shari'a ta kwamitin tsakiyar JKS Meng Jianzhu ya gabatar, yayin wani taron kara wa juna sani na yini biyu, kan harkokin mulki da ya gudana a ranekun Litinin da Talata.
Cikin sanarwar, shugaba Xi ya jaddada muhimmancin gina kasar Sin mai cikakken tsarin tsaro, da kuma managarcin jagoranci. (Saminu Hassan)