in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar harkokin wajen Sin ta kira taron manema labaru kan ziyarar da shugaban Sin zai yi a kasashen Cambodia da Bangladesh
2016-10-10 14:10:21 cri

A Litinin din nan ne ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta kira taron manema labaru, inda mataimakin ministan harkokin wajen kasar Li Baodong, da mai ba da taimako na ministan harkokin waje Kong Xuanyou, suka yi karin haske game da ziyarar da shugaban Sin Xi Jinping zai gudanar a kasashen Cambodia da Bangladesh, tare da halartar taron ganawa tsakanin shugabannin kasashen kungiyar BRICS karo na 8 a birnin Goa na kasar India.

Mr. Li Baodong ya ce wannan taron ganawa na da matukar ma'ana kasancewar irinsa na farko da shugabannin kasashen 5 za su gudanar, tun bayan da suka gana da juna a birnin Hangzhou na kasar Sin a watan jiya.

A gun taron, shugabannin kasashen kungiyar BRICS za su yi musayar ra'ayi kan lamuran kasa da kasa, da na yankuna, da kuma aikin hadin gwiwa a tsakaninsu. Daga bisani kuma za a bayar da sanarwar Goa, wadda za ta bayyana sakamakon da za a samu a yayin wannan taro.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China