Babbar jami'a mai kula da tsare tsare a sashen tattalin arzikin yankunan karkara da harkokin noma, ta ofishin kungiyar hadin kan Afirka AU, uwar gida Leah Naess Wanambwa, ta ce hukumar zartaswar AU na gudanar da aikin zakulo kwararru daga nahiyar Afirka, wadanda zasu taimaka wajen aiwatar da dabarun yaki da laifuka masu nasaba da mallaka da cinikayyar sassan namun daji da tsirrai ba bisa ka'ida ba.
Wanambwa wadda ta yi wannan tsokaci yayin taron kasa da kasa karo na 17, da aka shirya a birnin Johannesburg na Afirka ta kudu game da yaki da cinikayyar halittun dake daf da karewa daga ban kasa a jiya Talata, ta ce shirin wanda kasashen Afirka suka amince da shi, zai tallafa wajen dakile matsalolin da ake fuskanta a wannan fanni.(Saminu Alhassan)