in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude babban taron AU kan tsaron teku a Lome
2016-10-11 13:15:45 cri

Faraministan kasar Togo Selom Klassou ya jagoranci a ranar Litinin a birnin Lome, da bikin bude ayyukan daban na babban taron shugabanni da gwamnatocin kungiyar tarayyar Afrika (AU) kan tsaro da tsaron teku da kuma cigaba da ake kira "Side-events" da kasar Togo take karbar bakunci daga ranar 10 zuwa 15 ga watan Oktoba.

A cewar ministan harkokin wajen Togo, Robert Dussey, "Side-events" sun kasance wani jerin ayyuka na daban dake da manufar zama wani dandalin muhawara inda za a tattauna batutuwa da dama, musammun ma yaki da 'yan fashin taku da sumogal, tattalin arzikin gaggawa, kalubalolin tsaro da tsaron teku, matsalolin mallakar teku da musanya ta fuskar shari'a da 'yan sanda.

Side-events sun kunshi "kauyen dangantaka" da aka gina bisa muraba'in mita 2800 kana yana dauke da rumfunan baje koli 49. Kauyen dangantaka ya kunshi da wani zauren muhawara na muraba'in mita 400, dakin cin abinci na muraba'in mita 400 da wurin zaman manyan baki na muraba'in mita 200. Daga ciki masu baje kolin 49, kusan 21 sun fito daga kasashen waje.

A tsawon kwanaki hudu daga ranar 10 zuwa 14 ga watan Oktoba, mahalarta dandalin za su tattauna manyan batutuwan goma da masu shirya dandalin suka zaba, kana kwararru 238 da manyan jami'ai daga manyan jami'o'i da masu bincike za su halarci wannan dandali. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China