in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU: PRC yana sake nazarin dokokin tsaron tekun Afirka
2016-10-12 10:15:09 cri

Wakilan kwamitin din-din-din na kungiyar tarayyar Afirka(PRC) ya fara wata ganawa a birnin Lome na kasar Togo, da nufin sake nazartar daftarin dokar tsaron teku da harkokin ci gaba a nahiyar Afirka, dokar da ake sa ran gabatar da ita yayin taron shugabannin kungiyar AU a ranar 15 ga wannan wata don neman amincewarsu.

Shugaban kwamitin wakilan na PRC Cherif Mohamat Zene, ya ce, manufar sake nazarin daftarin ita ce, fito da wata managarciyar doka da za ta kawo karshen duk wata barazana da ake fuskanta a ruwayen kasashen da ke nahiyar, tsara matakan bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba, da fayyace dabarun tunkarar matsalar sauyin yanayi da illolin da suka shafi teku da matakan magance duk wasu bala'u da ke iya kunno kai da sauransu.

Bayanai na nuna cewa, da zarar an amince da wannan doka a taron na Lome, kasashen Afirka za su samu damar tsara ayyukansu, tare da hade dokokinsu waje guda, su kuma karfafa dabarunsu na sanya ido a ruwayen da ke yankunansu.

Kasashen nahiyar Afirka dai suna fama da matsalar tsaro a tekun Aden da na Guinea, inda kididdiga ke nuna cewa, nahiyar tana hasarar kimanin dala biliyan 7 a ko wace shekara.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China