Mai magana da yawun majalisar dokokin kasashen Afirka Roger Nkodo Dang ne ya bayyana hakan a jiya Talata. Ya kuma shaidawa taron manema labarai bayan ganawarsa da takwaransa na majalisar wakilan kasar Morocco Rachid Talbi Alami cewa, majalisar dokokin kasashen Afirka za ta taka rawar da ta dace wajen ganin ta hade kan nahiyar wuri guda. Mr Roger Nkodo ya yaba da shawarar da kasar Moroccon ta yanke na sake dawowa cikin kungiyar ta AU.
Tun a shekarar 1984, lokacin da ake kiran kungiyar da suna, kungiyar hada kan kasashen Afirka ne dai kasar ta Morocco ta fice daga cikin kungiyar. Kana a watan Yuli, Moroccon ta sanar da cewa, za ta sake dawowa cikin kungiyar tarayyar Afirka, shekaru 32 bayan ficewarta daga kungiyar sakamakon wata takaddama da ta shafi kasa.(Ibrahim)