Sa'an nan, a jiya Asabar, kungiyar AU ta fidda wata sanarwa, inda shugabar kungiyar Nkosazana Dlamini Zuma ta yi allah wadai da kakkauwar murya kan wannan mugun harin da aka kai, inda dakaru masu dauke da makamai kimanin guda 40 suka shiga yankin tsaro cikin motoci, tare da kashe sojoji guda 22 wadanda suke kula da tsaron sansanin, yayin da guda uku suka jikkata.
Haka kuma, madam Zuma ta nuna goyon bayan kungiyar AU ga gwamnati da al'ummomin kasar Nijer, tare kuma da nuna juyayi matuka ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.
Bugu da kari, ta sake jaddada aniyar kungiyar tarayyar Afirka wajen yaki da dukkan irin 'yan ta'adda da masu tsattsauran ra'ayi a nahiyar Afirka. (Maryam)