Nkosazana Dlamini-Zuma, ta bayyana hakan ne a Lome, babban birnin kasar Togo, a lokacin da take ganawa da kungiyoyin matan Afrika masu ruwa da tsaki a harkokin masana'antu na ruwa, a yayin taron kungiyar tarayyar Afrika kan sha'anin tsaro da ci gaban tekunan Afrika.
An dai saki wasu daga cikin 'yan matan na Chibok ne, bayan shafe sama da shekaru biyu ana garkuwa da su.
Shugabar ta AU ta bukaci al'ummar Najeriya da su tallafawa 'yan matan da aka sako domin komawa hayyacinsu don ci gaba da rayuwa cikin al'umma.
Dlamini-Zuma, ta nuna kyakkyawar fatarta na ganin an sako ragowar 'yan matan nan ba da jimawa ba. (Ahmad Fagam)