in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban taron MDD zai nada sabon sakatare janar na MDD a gobe Alhamis
2016-10-12 10:30:18 cri

Shugaban babban taron MDD karo na 71 Peter Thomsen ya aika da sakonni ga kasashe membobi a jiya Talata cewa, MDD za ta kira babban taronta a gobe Alhamis, domin nada Antonio Guterres don ya zama sabon babban magatakardan MDD.

Peter Thomsen ya bayyana cewa, babban taron MDD na gobe Alhamis zai gudana ne da karfe 10 na safe, ana fatan za a zartas da kudurin nada sabon babban magatakardan MDD ta hanyar yin tafi.

Peter Thomsen ya kara da cewa, babban taron MDD ya shirya wani kwarya-kwarya taro da yammacin ranar 19 ga wannan wata, wanda Antonio Guterres zai halarta, ana fatan wakilan kasashe membobi da kuma kungiyoyin shiyya-shiyya za su gabatar da jawabai.

Babban magatakardan MDD Ban Ki-moon zai kawo karshen wa'adin aikinsa ne a ranar 31 ga watan Disambar wannan shekara. Tun daga karshen shekarar bara ne aka fara shirye shiryen zabar sabon babban magatakardan MDD. Daga watan Yulin wannan shekara, kwamitin sulhu na MDD ya yi tarurukan jefa kuri'u sau 6, Antonio Guterres ne ya rika samun rinjaye. A ranar 6 ga watan Oktoba, kasashe membobi 15 na kwamitin sulhu na MDD sun amince da Antonio Guterres da ya zama sabon babban magakatardan MDD wanda zai maye gurbin Ban Ki-moon.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China