Kwamiti na biyu na babban taron MDD karo na 71 mai kula da warware matsalolin tattalin arziki ya gudanar da wani taro game da yadda za a gudanar da ayyukansa a jiya Alhamis. A cikin jawabin da ya gabatar wajen taron, Wu Haitao ya bayyana cewa, kamata ya yi a dora muhimmanci ga batun bambancin bunkasuwar kasashe matsakaita, da sa kaimi ga samun bunkasuwa tare, yayin da ake gudanar da ayyukan kwamitin.
Wu Haitao ya bayyana cewa, MDD ta taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da ajandar samun bunkasuwa mai dorewa nan da shekarar 2030, don haka kamata ya yi a tsara buri da shirye-shiryen aiwatar da ayyuka, da dora muhimmanci ga batutuwan kawar da talauci, da tinkarar bala'in dake aukawa halittu, da matsalar sauyin yanayi, da kiwon lafiya da dai sauransu.
Wu Haitao ya kara da cewa, ya kamata kasashe masu ci gaba su cika alkawarinsu na bada gudummawa, yayin da kasashe masu tasowa ya kamata su kara hadin gwiwa da juna, don taimakawa wajen raya hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa da masu wadata. (Zainab)