Mambobin babban taron MDD 193 ne suka amince da kudurin nadin nasa, bayan da jakadan kasar Rasha dake MDD, Vitali Tchourkine kana shugaban kwamitin sulhu na MDD na watan Oktoba, ya sanar da taron MDD wannan shawarar bayan da ya samu goyon bayan kwamitin game da nadin mista Guterres.
A ranar ga watan Janairun shekarar 2017 ne zai fara wa'adin aikinsa na shekaru biyar, kuma wa'adin zai kare a ranar 31 ga watan Disamban shekarar 2021. Cikakken dan siyasa mai shekaru 67 da haifuwa, mista Guterres ya rike mukamin babban kwamishinan hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD daga watan Yunin shekarar 2005 zuwa watan Disamban shekarar 2015. Kafin ya rike shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD, mista Guterres ya kwashe tsawon shekaru 20 yana aiki a gwamnatin kasar. Ya kuma zama faraministan Portugal daga shekarar 1995 zuwa shekarar 2002. (Maman Ada)