Babban magatakardar MDD Ban Ki Moon, ya yaba da tagomashi da takarar tsohon firaministan kasar Portugal Antonio Guterres ke samu, a kokarin sa na samun amincewa ya zama sabon babban magatakardar MDD.
Mr. Ban ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, bayan ganawar sa da shugaban kasar Italiya Sergio Mattarella. Ya ce ya fahimci Guterres matuka, yana kallon sa a matsayin managarcin jagora.
Babban magatakardar MDDr ya kara da cewa Guterres na da matukar kwarewa a matsayin sa na tsohon firaminista, ya kuma yi aiki a fannin diflomasiyya a wurare da dama, matakin da zai bashi damar jagorantar MDD nan da shekaru 5 masu zuwa, wato tun daga ranar 1 ga watan Janairun shekara mai zuwa.
A jiya Alhamis din ne kuma kwamitin tsaron MDD ya tabbatar da Guterres a matsayin dan takarar sa a hukunce. Guterres, dan shekaru 67, ya jima yana rike da shugabancin hukumar MDD mai kula da 'yan gudun hijira wato UNHCR.(Saminu Alhassan)