Bikin makon Afirka ya gudana a wannan rana a cibiyar MDD, bikin da aka yiwa lakabi da "kara raya dangantakar abokantaka ta samun bunkasuwa mai dorewa, da gudanar da ayyukan siyasa mai dacewa da wanzar da zaman lafiya a nahiyar Afirka".
A gun bikin bude taron, Mr. Liu Jieyi ya gabatar da jawabi, wanda a cikin sa ya bayyana cewa, kamata ya yi a aiwatar da ajendar samun bunkasuwa mai dorewa ta shekarar 2030, da ajendar shekarar 2063 ta nahiyar Afirka, a kuma maida hankali ga cimma burin kawar da talauci da yunwa, da kara hadin gwiwa a fannin samar da kayyayaki a yankin, da sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma, da kiyaye muhalli a nahiyar Afirka.
Ya ce, ya kamata a tsaya tsayin daka kan ka'idar aiwatar da mnufofi masu dacewa da ra'ayoyin kasashen nahiyar, da nuna goyon baya ga kasashen ta, ta yadda za su tsara manufofin samun bunkasuwa da za su dace da yanayinsu. (Zainab)