A jiya Jumma'a ne asusun makamashi na kasar Sin dake Hongkong, ya gudanar da dandalin tattaunawa game da makamashi, da tsarin zirga-zirga mai dorewa, inda aka gayyaci wasu jami'an MDD da kwararru a fannin makamashi, domin ba da jawabai da tattauna kan aikin cimma burin neman dawamammen ci gaba, da kuma kafa tsarin zirga-zirga mai dorewa.
Mataimakin babban magatakardan MDD Wu Hongbo ya ba da jawabi a gun bikin bude taron. Inda ya ce yunkurin bunkasuwa mai dorewa nan da shekarar 2030 ya shafi ko wane mutum, kuma taswira ce ta neman samun dauwamammen ci gaba ga bil Adama. Ya ce, ya kamata kowa ya ba da gudummawa wajen cimma wannan buri.
Mr. Wu ya kara da cewa, kafa tsarin zirga-zirga mai dorewa wani muhimmin aiki ne ga MDD. Ya ce, nan da shekarar 2050, mutane biliyan 2.5 za su kaura zuwa birane a duniya, musamman ma a nahiyoyin Asiya da Afrika. Domin tinkarar wannan hali, dole ne a yi bincike kan makamashi da tsarin zirga-zirga gaba daya, wajen warware batutuwan habakar birane wato alal misali cunkoson motoci da gurbata iska a sakamakon zirga-zirga.
Daga nan sai ya yi kira ga kasashe daban daban da su yi koyi da juna wajen daidaita batutuwan zirga-zirga da na makamashi.(Lami)