in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
RDC-Congo: CENI ta gabatar da wa'adin kwanaki 504 domin shirya zabuka
2016-10-02 12:18:50 cri
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (CENI), Corneille Nangaa, ya gabatar a ranar Asabar da wani jadawali na kwanaki 504 domin shirya zabuka a jamhuriyar demokuradiyyar Congo.

A cewar shugaban CENI, wannan wa'adi na farawa daga watan Febrairun wannan shekara, domin baiwa musammun ma damar tanadar kayayyakin zabe, har ma kuma kammala ayyukan kawo gyaran fuska ga rejistan zabe da sauran ayyukan da suka jibanci wannan aiki.

Mista Corneille Nangaa ya gabatar da wannan jadawalin a yayin wani taron bada lacca da aka gudanar a zauren "Cite de l'OUA" dake Kinshasa, gaban mahalarta taron tattaunawar siyasa da shugaba joseph Kabila ya kira, a karkashin jagorancin kungiyar tarayyar Afrika (AU).

Mai gabatarwa na biyu na bangaren 'yan adawa a taron tattaunawar siyasa, Vital Kamerhe ya bayyana cewa a shirye suke su amince da gudanar da zabuka a cikin watan Satumban shekarar 2017, kana ba bayan wannan lokaci ba.

Ana kira ga daukacin wakilan dake halartar wannan tattaunawa dasu daidaita ra'ayoyinsu kan shawarar da shugaban CENI ya gabatar, domin samun hanyar fita daga wannan matsala, in ji mista Vital Kamerhe.

Matsalar gudanar da zabuka a cikin wa'adi na kawo rarrabuwar kawuna sosai a dandalin siyasar RDC-Congo, a yayin da wasu masu adawa da shugaba mai ci Joseph Kabali da neman lakewa a kan mulki baya ga wa'adin mulkinsa da zai karewa a wannan shekara. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China