in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
RDC-Congo: Kawancen Jam'iyyu masu rinjaye sun nuna damuwa kan matakin MDD ta dauka na sanya kasar karkashin sa ido
2016-10-03 12:20:22 cri
Kawancen Jam'iyyu masu rinjaye (MP) na nuna damuwa matuka bayan matakin da MDD ta dauka na sanya RDC-Congo karkashin sa ido bisa dalilin tashe tashen hankalin da suka faru a cikin watan Satumba, in ji Alain Atundu, kakakin kawancen, a yayin wani taron manema labarai da ya gudana a ranar Lahadi a birnin Kinshasa.

Wannan mataki na yin allawadai na tabbatar cikin takaici da muguwar dabi'ar kungiyoyin MDD na gudanar da bincikensu na tura laifi kawai ga hukumomi masu cikakken iko dake gudanar da mulki bisa tsarin kundin kasa, in ji mista Atundu.

A cewar jami'in, mantawa cikin mamaki bisa wata manufa ta daban da laifuffukan shugabannin kawancen 'yan adawa kan abubuwan da suka faru, bisa ganin yadda shugabansu yayi alkawari da sanarwar dawowa fagen siyasa da karfin damtse a ranar 19 ga watan Disamba, ba su taimakawa ko kadan wajen kafa wani yanayin kwanciyar hankali cikin kasa, kamar yadda sakatare janar na MDD yake shelanta cewa, in ji mista Atundu.

Fiye da mutane 30 aka kashe a ranakun 19 da 20 ga watan Satumba a Kinshasa a lokacin zangar zangar kawancen 'yan adawa a yayin fito na fito tare da jami'an tsaro. Inda aka wawushe shaguna da bankuna, kana aka kone wasu hedkwatocin jam'iyyun adawa da na masu rinjaye a lokacin tashe tashen hankalin. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China