in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a gyara dokar maida kadarori ga 'yan kasa dake fuskantar takaddama a Zimbabwe, in ji shugaban kasar
2016-10-08 12:31:21 cri
A kwanan baya, shugaban kasar Zimbabwe Robert Gabriel Mugabe ya bayyana cewa, za a yi gyaran fuska ga dokar mika kadarori ga 'yan kasa a majalisar dokokin kasar, ta yadda za ta dace da gyare-gyaren da ake yiwa manufofin kasar.

A shekarar 2007, kasar Zimbabwe ta zartas da daftarin dokar maida kadarori ga 'yan kasa, ko dokar sauya izinin mallakar tattalin arziki. Dokar ta bukaci kamfanonin da karfin kadarar su ya kai sama da dallar Amurka dubu dari biyar, kuma wadanda suka sami jari daga ketare, ko kuma wadanda suke karkashin mallakar Turawa, da su mika babban kaso na ikon jarin su, watau a kalla kashi 51 bisa dari na kamfanoninsu ga 'yan kasa.

Amma cikin shekaru da dama da suka gabata, sabo da hukumomin gwamnatin kasar ba su cimma ra'ayi daya kan wannan batu ba, shi ya sa an kasa gudanar da ayyukan da abin ya shafa kamar yadda aka fata.

Dangane da wannan lamari, shugaban kasar ya bayyana cewa, sakamakon gaza cimma ra'ayi daya kan wannan batu, an fuskanci koma baya ga bunkasuwar kasuwannin kasar.

Wasu manazarta na ganin cewa, dokar maida kadarori ga 'yan kasa za ta haddasa raguwar jarin da kasar ke samu daga ketare, lamarin da zai haddasa karin matsaloli wajen farfado da tattalin arzikin kasar. Sai dai wasu shugabannin gwamnatin kasar na ganin cewa, dokar za ta tabbatar da tallafa wa al'ummomin kasar ta wannan hanya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China