in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harkokin kasuwanci ya gurgunce a manyan biranen kasar Zimbabwe sakamamkon yajin aiki
2016-07-07 10:04:52 cri
Harkokin kasuwanci sun sakwarkwace a Harare, babban birnin kasar Zimbabwe da wasu manyan biranen kasar tun daga jiya Laraba, hakan ya biyo bayan nasarar da shafukan sada zumunta na kasar suka yi ne, inda suka bukaci jama'ar kasar da su zauna a gidajensu domin nuna adawa game da yadda tattalin arzikin kasar ya durkushe.

Yajin aiki na ranar Laraba, ya kasance wani mummunan yanayi da kasar da shafe shekaru fiye da goma ba ta ga irinsa ba, sannan ya zo daidai da rana ta biyu da malaman makarantun kasar, da ma'aikatan lafiya ke gudanar da yajin aiki a sakamakon jinkirin biyansu albashi. Sannan ya kasance kwanaki biyu bayan wani rikici da ya kaure tsakanin 'yan sandan kasar da direbobin kananan motoci a birnin Harare.

Shi dai wannan yajin aiki ya samo asali ne bayan sakonnin da aka dinga turawa ta wasu shafukan sada zumunta, inda ake umartar jama'a da su zauna a gidajensu, wasu sakonnin kuma na yin barazanar cewa kada a je wuraren aiki, ko kuma kai yara makarantu, inda ake gargadin cewar za'a iya kona motocin iyayen da suka yi yunkurin kai 'ya'yansu makarantun.

To sai dai har yanzu ba'a tantance dalilan da suka sa jama'ar suka ci gaba da zama a gidajensu ba, ko saboda amsa kiraye kirayen ne, ko kuma saboda fargabar yiwuwar barkewar tashin hankali, mafi yawan shaguna, da gidajen sai da abinci, da ofisoshi a babban birnin sun kasance a rufe, sai dai bankuna da wasu daga cikin ma'aikataun gwamnati sun kasance a bude. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China