in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zimbabwe za ta kafa dokar hukunta masu karya doka a shafukan yanar Gizo
2016-08-08 13:02:55 cri

Mahukuntan kasar Zimbabwe sun lashi takobin kafa sabuwar dokar hukunta masu karya ka'idojin kasar a shafukan yanar Gizo, dokar da za ta kushi daurin shekaru 5 a gidan kaso ga duk wadanda suka keta ta.

Rahotanni na cewa karkashin wannan doka, za a hukunta duk 'yan kasar dake zaune a Zimbabwe, ko ma a ketare, dake amfani da dukkanin wasu nau'o'i na bayanai a kafofin sadarwar zamani domin cin zarafi, ko tsoratarwa, ko tada hankalin wasu.

Rahotanni na cewa dokar wadda za ta samu goyon bayan wasu sassan dokokin dake kunshe cikin kundin tsarin mulkin kasar, na da nufin dakile ayyukan bata gari, dake amfani da yanar gizo ko shafukan zumunta, wajen aikata laifuka, tare da magance dadaddiyar matsalar rashin da'a da wasu ke aikatawa ta amfani da yanar gizo.

Dokar dai na zuwa ne bayan da a 'yan kwanakin nan, wasu kungiyoyin 'yan adawar kasar suka rika amfani da kafafen sadarwa na zamani irin su shafukan sada zumunta, wajen tunzura jama'a da shirya bore a cikin kasar, matakin da suka danganta da nuna adawa da mawuyacin halin tattalin arziki, da cin hanci da rashawa dake addabar al'ummar kasar. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China