in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Zimbabwe ya yi wa 'yan adawa kashedi kan neman tada fitina cikin kasa
2016-08-27 12:44:12 cri
Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya yi kashedi a ranar Jumma'a ga jam'iyyun adawa kan neman tada fitina cikin kasa.

Mista Mugabe ya yi wannan furuci ne a lokacin da 'yan sandan kasar suka tarwatsa wata zanga zangar 'yan adawa dake neman ganin an kawo gyaran fuska ga ayyukan zabe kafin zabukan shekarar 2018, wanda ta kasance cikin jerin zanga zangar 'yan adawa da kungiyoyin fararen hula domin nuna adawa da gwamnati a 'yan makwannin baya bayan nan.

A ko wane lokaci, 'yan sanda na amfani da barkonon tsofuwa da mesar ruwa domin tarwatsa masu zanga zanga.

'Yan adawa ba za su taba samun mulki ba ta hanyar gudanar da zanga zanga da tashe tashen hankali, in ji shugaba Mugabe, tare da danganta matsalolin tattalin arzikin kasarsa na yanzu ga takunkumin yammacin duniya da suka sanya wa kasar da kuma fari.

Da yake zargin kasashen yammacin duniya da sanya hannu kan wadannan zanga zangar 'yan adawa, mista Mugabe ya nuna cewa gwamnatinsa ba za ta rufe ido ba kan duk wasu tashe tashen hankali cikin kasa.

Ba mu bukatar a nuna ma rashin girmamawa. Mu mutane ne masu son zaman jituwa kana muna son zaman lafiya a cikin kasarmu, in ji Robert Mugabe. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China